Mace Da Kisan Gilla A Taskar Adabi: Tsokaci A Cikin Wasu Waƙoƙin Hausa Na Zamani

    Tsakure: Ɗabi’ar kashe mazaje da matan wannan zamani kan yi wata sabuwar al’ada ce da ta samu kuma abin takaici. Dangane da haka ne aka sami wasu mawaƙan zamani waɗanda suka samar da waƙoƙi game da matsalar. Wato Mawaƙi Abubakar Sani ɗan asalin Jihar Kano da kuma Isa Sani Ranɗawa, ɗan asalin Jihar Katsina.  Ganin cewa ba a ga wani nazari a kan wannan ɗabi’a daga waƙoƙin da waɗannan mawaƙa biyu suka yi ba, ya sa aka zaɓi a yi tsokaci a kansu. Manufar wannan maƙala ita ce, ta fito da gudummawar waɗannan mawaƙa a fagen ilimi domin alumma su amfana. Ko ba komai an yarda da cewa adabi hoto ne na rayuwar al’umma. Maƙalar ta saurari waƙar da kowannensu ya yi, tare da tattaunawa da mawaƙan, ta tace muhimman bayanai daga gare su. Ta haka ne wannnan maƙala ta fito da ɗabi’ar kisan gilla a waƙar da Abubakar Sani ya yi ta hanyar nuna takaicinsa da lallashin mace da tsoratar da ita domin ta guje wa ɗabi’ar. A waƙar da Isa Sani Ranɗawa ya yi kuma aka fito da wasu dalilan da ya ce su suke saka mata su kashe mazajensu na aure domin ya jawo hankalin maza a kan nasu kurakuren tare da tsoratarwa ga mata a kan sakamakon aikata ɗabi’ar ko da kuwa an saɓa masu ne. Daga ƙarshe an gano cewa waɗannan mawaƙa sun fito da gaskiyar abin da yake faruwa ne a cikin alummar da suke rayuwa, wato ba shaci-faɗi kawai irin na adabi ba. Sannan an gano cewa, waƙoƙin ba su kasance masu tunzura mata ba, face faɗakarwa kurum domin mace Bahaushiya ta ci gaba da kasancewa mai mutunci a idon duniya kamar yadda aka san ta. Haka kuma, domin su maza su sauya taku wajen zama da mace, su fahimci cewa jiya ba yau ba ce.

    Fitilun Kalmomi: Mace, Kisan Gilla, Taskar Adabi, Waƙoƙin Hausa, Zamani

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.061

    Download the article:

    author/Rabi Mohammed

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages