Tsakure:
Masu hikima na yin amfani da adabin baka wajen sarrafa harshen Hausa don sauran mutane masu magana da kuma amfani da harshen Hausa su saurara su kuma more wajen samun zantuttuka masu armashi da ke kawo nishaɗi da birgewa. A wannan takarda an yi amfani da ɗaya daga cikin waɗannan sassa na adabi wajen fito da wasu daga cikin tarin muhimmancin da suke da su ta fuskar kawo faɗakarwa don kawo gyara da ɗora al’umma a kan hanyar aikata abubuwan da suka kamata da gujewa munanan ayyuka. Don haka an yi amfani da rubutattun waƙoƙi don nuna irin tasirin da suke da su wajen faɗakarwa a waɗannan lamuran da suka danganci zamantaker Hausawa ta yau da gobe.
Fitilun Kalmomi: Rubutattun Waƙoƙi, Faɗakarwa, Zamantakewa, Hausawa
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.014
author/Tijjani Muhammad Salihi
journal/GNSWH, April 2024