Tsakure:
Wannan bincike mai taken: “Balbela Ba Ta Bin Kare Sai Shanu: Al’adar Roƙo da Ƙunshiyarta a Bakin Mawaƙan Baka na Hausa.” An gina shi da manufar laluben ƙunshiyar al’adar roƙo a bakunan mawaƙan baka na Hausa. Binciken ya yi ƙoƙarin waiwayar ayyukan da magabata suka gudanar masu alaƙa da roƙo, domin ganin inda suka tsaya, saboda a san inda za a tunkara. Wasu daga cikin hanyoyin da binciken ya yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Hausa na baka daga bakin maƙagansu, waɗanda aka taskance su a na’urar adana bayanai ta memori. Haka kuma, nazarin ya bibiyi wasu daga cikin waƙoƙin baka da aka rubuta a wallafaffun littattafai domin daidaita abin da aka saurara na muryoyin mawaƙan da kuma abin da yake a rubuce. Har wa yau, an tuntuɓi wasu ɗaiɗaikun manazarta da suke da masaniya a kan batun da ake bincike a kan sa, saboda buƙatar da ake da ita ta samun hasken da zai ƙara wa maƙalar tagomashi. An yi amfani da Bahaushiyar hanyar ɗora aiki wadda ke cewa: “Kowace Ƙwarya Tana da Abokiyar Burminta.” Binciken ya yi garkuwa da ɗiyan waƙoƙi 26 daga bakunan mawaƙa daban-daban guda 12 a matsayin misalai. A ƙarshe, takardar ta gano cewa, akwai hanyoyi da yawa da mawaƙan baka na Hausa suke amfani da su domin bayyana abin da suke roƙo a wurin waɗanda suke wa waƙa. Kamar yadda nazari ya ƙyallaro cewa, mawaƙan sun fi roƙon abubuwan da suka shafi abin hawa (mota ko doki) da kuɗi da hajji da sutura (tufafi) da gida da gona da abinci da kuma sauran abubuwan da rayuwar ɗan’adam ke buƙata.
Fitilun Kalmomi: Balbela, kare, shanu, al’ada, roƙo, da mawaƙan baka